logo

HAUSA

Kwamitin rikon kwarya da maido da ayyukan hukumomi a Gabon ya sanar da bude kan iyakokin kasar

2023-09-02 21:20:38 CMG Hausa

Kwamitin rikon kwarya da maido da ayyukan hukumomi a Gabon ko CTRI, ya sanar da bude kan iyakokin kasar na kasa, da ruwa, da sama tun daga Asabar din nan.

Kwamitin na CTRI, wanda ya bayyana matakin ta wata sanarwa da aka watsa ta kafar talabijin din kasar, ya ce matakin na da nasaba da burin da ake da shi na ingiza ci gaban kasar, tare da martaba alkawuran Gabon ga yarjeniyoyin kasa da kasa.   (Saminu Alhassan)