An gurfanar da firaministan Japan gaban kuliya
2023-09-02 16:14:29 CMG Hausa
Jiya Juma’a, wata kungiya mai zaman kan ta ta al’ummar Japanawa da ake kira “kungiyar tuntubar juna, kan yaki da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku”, ta gurfanar da firaministan kasar Fumio Kishida, da shugaban kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo a gaban kotu, don nuna rashin jin dadinsu game da matakin zubar da ruwan dagwalon nukiliya da jami’an suka amince a yi, ba tare da yin la’akari da ra’ayin jama’a ba.
Kungiyar ta ce, ruwan da aka sarrafa na kunshe da sinadarai masu guba, wadanda ba a cire su ba. Kuma matakin da gwamnatin ta dauka na cike da kuskure. (Amina Xu)