logo

HAUSA

AU ta sanar da dakatar da Gabon a matsayin mambanta

2023-09-01 10:49:01 CMG

A ranar 31 ga Agusta ne kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afirka AU, ya gudanar da wani taro kan halin da ake ciki a kasar Gabon, inda ya yi kakkausar suka kan juyin mulki da wasu sojoji suka yi a Gabon tare da hambarar da shugaba Bongo na Gabon. Kungiyar ta AU ta yanke shawarar dakatar da kasar Gabon daga zama mambanta kuma ta hana ta shiga duka harkokin kungiyar, da kuma sauran hukumomi da ke da alaka da ita har sai an maido da tsarin mulkin kasar ta dimokuradiyya. (Yahaya)