logo

HAUSA

Goyon bayan da Amurka ta baiwa Japan game da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba shi da amfani

2023-09-01 21:32:47 CMG Hausa

Jiya Alhamis, jakadan Amurka dake Japan, ya kai ziyara Fukushima inda ya dandana wasu abincin teku a wuri, don nuna goyon baya ga gwamnatin Japan, kan batun zubar da ruwan dagwalon nukiliyar ta cikin teku.

Ban da wannan kuma, wannan jakada ya tsoma baki kan matakin da ya dace da Sin ta dauka, a shafinsa na sada zumunta na Intanet. To sai dai kuma a wannan rana, jami’i mai kula da kayayyakin gona da teku na Japan, ya kira ruwan da gwamnatin Japan ta zuba cikin teku da sunan gurbataccen ruwan nukiliya, yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa. Game da hakan, an ce, ba kurkure wannan jami’i ya yi ba, gaskiya ce ya fada.

Jami’an Japan sun amince cewa, wannan ruwan da aka zuba gurbatacce ne, don haka goyon bayan da Amurka ke yiwa gwamnatin Japan ya zama abun dariya. Amma, abu mafi girgiza rai shi ne, bisa kididdigar da hukumar kayayyakin gona da teku ta Japan ta bayar ta nuna cewa, Amurka ta kasance kasa da ta fi rage shigo da albarkatun teku daga Japan, abinci uku da Amurka ta kayyade shigar da su cikin kasar, Fukushime ne ke samar da su. Ba shakka wannan ya nuna cewa, goyon bayan da Amurka ke yiwa gwamantin Japan kan wannan batu, abun dariya ne kuma ba shi da amfani, kana ba wanda zai amince da shi. (Amina Xu)