logo

HAUSA

Shugaban Iran: SCO da BRICS za su magance danniya da nuna son kai a duniya

2023-09-01 15:33:58 CMG Hausa

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya bayyana cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da tsarin BRICS suna ba da gudummawa wajen tinkarar tsarin yin babakere da nuna son kai a duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne jiya Alhamis, a yayin wata ganawa da ya yi da wasu malamai da masana mashabar Sunna a Tehran, babban birnin kasar Iran, kamar yadda wata sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon fadar shugaban kasar ta bayyana.

Raisi ya ce, a halin yanzu, yayin da manyan kasashen duniya suka fuskanci koma baya, musamman Amurka, yanayin duniya yana sauyawa.

Ya kara da cewa, kungiyar SCO da tsarin BRICS, dukkansu tsare-tsare ne dake da nufin tinkarar matakan dannayi da nuna son kai. 

A ranar 24 ga watan Agusta ne, aka gayyaci kasashen Iran da Argentina, da Masar, da Habasha,da Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa a hukumance, don shiga kungiyar BRICS, kungiyar kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da suka hada da kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, da Afirka ta Kudu.

A farkon watan Yuli, Iran ta zama cikakkiyar mamba a kungiyar SCO a yayin taron kungiyar majalisar shugabannin kasashen kungiyar karo na 23. (Ibrahim Yaya)