logo

HAUSA

An haramtawa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu yin aiki a yankuna da ayyukan soja ke gudana a Nijar

2023-09-01 10:42:27 CMG

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Nijar ta sanar a ranar Alhamis cewa, an hana hukumomin majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu yin aiki a “shiyyoyin da aikin soja ke gudana”

Hakan ya faru ne a dalilin halin da ake ciki na tsaro da kuma yadda rundunar sojojin Nijar ke ci gaba da gudanar da ayyukanta, a cewar ma'aikatar.

Nijar dai tana fama da ta'asar kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da kungiyoyi masu dauke da makamai da masu aikata laifuka da suka mamaye kudancin kasar Libiya tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Gaddafi a shekara ta 2011. Haka kuma akwai kungiyoyin 'yan ta'adda da ke da sansani a arewacin kasar Mali.

A cikin ‘yan shekarun nan, wata sabuwar cibiyar ‘yan ta’adda ta kunno kai a yankin kudu maso yammacin Nijar, yankin da ake kira “iyakoki uku” wato yankin da ta hade iyakokin Nijar da Mali da Burkina Faso inda kungiyoyin ‘yan ta’adda su kan kai munanan hare-hare kan sojoji da fararen hula. (Yahaya)