logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin da Korea ta Kudu sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kasashensu

2023-09-01 14:22:55 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Korea ta Kudu Park Jin, a jiya Alhamis. 

Yayin tattaunawar wadda ta gudana bisa gayyatar Park Jin, Wang Yi ya ce manufar kasar Sin kan Korea ta Kudu na ci gaba da gudana kuma bisa kwanciyar hankali. Yana mai cewa, kasashen na da karfin raya dangantakarsu dake da muhimmiyar ma’ana, kuma bai kamata wani bangare daga waje ya yi tasiri cikinta ba. 

Ya kuma bayyana fatan Korea ta Kudu za ta karfafa cikakken ’yancinta da watsi da dukkan yunkurin dake adawa da dunkulewar duniya da na raba gari ko lalata tsarin samar da kayayyaki, tare da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da Sin a bangarori mabanbanta, ta yadda za su kara kawo alfanu ga jama’ar kasashen biyu.

A nasa bangare, Park Jin ya ce Korea ta Kudu ba ta da niyyar raba gari da wata kasa dangane da batun samar da kayayyaki. Yana mai cewa raba gari da kasar Sin ba abu ne da ake muradi ba, baya ga kasancewarsa mara yiwuwa.

A cewarsa, a shirye Korea ta Kudu take ta zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da Sin, da kuma tabbatar da tsarin samar da kayayyaki bai gamu da tangarda ba, tare da hada hannu wajen raya tattalin arzikin shiyyarsu. (Fa’iza Mustapha)