logo

HAUSA

Sharhi:Bai kamata a manta da abin da ya faru a Kabul ba

2023-08-31 21:32:06 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Shekaru biyu ke nan, tun bayan da Amurka ta janye sojojinta daga kasar Afghanistan. A ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2021, jirgin saman soja na karshe na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman birnin Kabul, wanda ya dasa aya ga yakin Afghanistan da aka kwashe tsawon shekaru 20 ana yinsa.

Yakin da Amurka ta kaddamar a Afghanistan cikin shekaru 20 da suka wuce, ya lalata kasar tare da makomar al’ummarta, tare kuma da hallaka mutane dubu 174, ciki har da fararen hula sama da dubu 30, baya ga kuma miliyoyin al’ummar kasar da suka zama ‘yan gudun hijira.

Duk da cewa Amurka ta janye sojojinta daga Afghanistan, amma har yanzu tana kakabawa kasar takunkumin tattalin arziki, tare da kwace kudade daga al’ummar kasar, matakan da suka jefa kasar cikin matsalolin jin kai.

A kwanakin baya, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da wani rahoto na tantance matakan da Amurka ta dauka, na janye sojojinta daga Afghanistan, wanda ya yi suka game da yanayi na rashin tsari da oda wajen kwashe sojojin, amma ba tare da bayyana ainihin abubuwan da ya kamata gwamnatin Amurka ta yi tunani a kansu ba.

Kaddamar da yaki a kan wata kasa mai mulkin kanta, abu ne da ya keta dokokin kasa da kasa, amma ko me ya sa rahoton bai yi bayani a kan hakan ba? Dubun dubatar fararen hula sun hallaka, ko jikkata a sakamakon yakin na tsawon shekaru 20, baya ga tabarbarewar yanayin tsaro da zaman lafiya a yankin. Ko me ya sa rahoton bai yi bayani a kan hakan ba? Amurka ta fake ne da sunan “wanzar da dimokuradiyya”, wajen tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe, amma me ya sa rahoton bai yi bayani a kan hakan ba?

Ba shakka, al’ummun duniya ba za su yi na’am da rahoton ba.

Amurka na daukar kanta a matsayin misali wajen kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya, amma ga abin da ta haifar a Afghanistan, da ma sauran sassan duniya. Idan ba ta daina daukar matakai na nuna fin karfi, da ma gyara yadda take tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe yadda ta ga dama ba, to, ba shakka, abin da ya faru a Afghanistan zai ci gaba da faruwa a sauran sassan duniya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)