logo

HAUSA

Shigar sabbin mambobi kungiyar BRICS za ta bada damar kara jin amon kasashen Afrika

2023-08-31 11:13:05 CMG Hausa

Tsohon wakilin kasar Habasha a MDD Teruneh Zenna, ya ce gayyatar da aka yi wa Habasha da Masar ta shiga kungiyar hadin gwiwa ta BRICS, za ta kawo sauyi ga nahiyar Afrika tare da bayar da damar kara jin amon nahiyar a dandamalin kasa da kasa.

A ranar 24 ga wata ne wani taron manema labarai na musamman na taron shugabannin BRICS karo na 15, ya sanar da gayyatar kasashen Saudiyya da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Argentina da Iran da Habasha, su zama mambobin kungiyar a hukumance.

Teruneh Zenna ya bayyana yayin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sabbin mambobin za su taimakawa kungiyar BRICS wajen kara tabbatar da adalci a duniya, kuma shigar wadannan kasashe, zai ba su kansu damar warware matsalolin da suke fuskanta kamar na rashin aikin yi da fatara. 

Har ila yau, ya ce gayyatar Habasha da Masar domin su shiga kungiyar gagarumar dama ce ga kungiyar BRICS wajen jagorantar kasashen Afrika ta fuskar neman karin adalci da daidaito a harkokin duniya. Kana sabbin mambobin za su hada hannu da tsoffin mambobin wajen kara yin kyakkyawan tasiri a shiyyoyinsu mabambanta. (Fa’iza Mustapha)