logo

HAUSA

Ana Zura Ido Kan Yadda Amurka Za Ta Ki Raba-gari Da Kasar Sin

2023-08-31 11:11:18 CMG Hausa

Jiya Laraba ne ministar kasuwancin kasar Amurka Gina Raimondo ta kammala ziyarar aikinta na kwanaki 4 a kasar Sin, wadda ita ce babbar jami’ar Amurka ta hudu da ta ziyarci kasar Sin tun daga watan Yunin bana.

Dangane da ziyararta, akasarin ra’ayoyin jama’a sun mai da hankali kan yadda Sin da Amurka suka sanar da kafa sabuwar hanyar tuntubar juna, matakin da suke ganin cewa, zai taimaka wajen rage rashin fahimtar juna a tsakanin kasashen 2. Kana Madam Raimondo ta bayyana a fili cewa, Amurka ba ta neman raba-gari da Sin, tare da fatan kamfanonin Amurka za su zuba jari a kasar Sin.

Masana sun bayyana wa wakilin CMG cewa, sabuwar hanyar tuntubar juna tsakanin Sin da Afirka, za ta taimakawa kasashen 2 wajen inganta tuntubar juna da mu’amalar juna, amma yadda sabuwar hanyar tuntubar junar za ta yi aiki yadda ya kamata, zai danganta da abin da Amurka za ta yi.

Ana fatan Amurka za ta aiwatar da kudurin kin raba-gari da Sin, ba kawai domin ci gaban huldar cinikayya a tsakanin kasashen 2 ba, har ma domin biyan bukatun sassan masana’antu da kasuwanci na kasashen 2, lamarin da zai amfana wa bunkasar tattalin arzikinsu da ma na duniya baki daya. Abin da ya zama wajibi Amurka ta yi yanzu shi ne, hanzarta soke harajin da take kara dora wa kasar Sin, dakatar da takunkumin da take sanyawa kayayyakin kasar Sin, da soke takunkuminta kan kamfanonin kasar Sin, a kokarin ganin kamfanonin kasashen 2 sun kara yin ciniki, zuba jari da hada kai.

Huldar tattalin arziki da cinikayya, tushe ne na huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka. Ana fatan sabuwar hanyar tuntubar junar za ta kasance a matsayin sabon mafari. Wato fatan Amurka za ta nuna sahihanci wajen daidaita matsaloli, za ta dauki matakai kamar yadda kasar Sin ta yi, za ta kara azama kan kyautata hulda a tsakaninta da Sin, da farfadowar tattalin arzikin duniya. Bayan ziyarar Raimondo, kasashen duniya na zura ido kan matakin da Amurka za ta dauka. (Tasallah Yuan)