logo

HAUSA

Mahukuntan Janhuriyar Nijar sun umarci Jakadan Faransa da ya fice daga kasar

2023-08-31 21:38:49 CMG Hausa

A yau Alhamis ne ma’aikatar harkokin wajen janhuriyar Nijar, ta fitar da wasu takardu dake cewa jakadan Faransa a kasar ba zai sake cin gajiyar kariya, da sauran hidimomin diflomasiyya da ake ba shi a ofishin jakadancin kasar ba. Kaza lika gwamnatin Nijar din ta umarci rundunar ‘yan sandan kasar da ta kori jakadan daga kasar. (Saminu)