logo

HAUSA

An nada Oligui Nguema a matsayin shugaban kasar Gabon

2023-08-31 10:14:53 CMG Hausa

An nada Brice Oligui Nguema, babban kwamandan rundunar tsaron kasar Gabon, a matsayin shugaban kwamitin mika mulki da maido da hukumomi (CTRI), kuma shugaban rikon kwarya, a jiya Laraba, biyo bayan juyin mulkin da ya hambarar da zaben Ali Bongo wanda hukumar zaben kasar ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.    

A farkon ranar ne, wasu daga cikin dakarun sojin kasar suka yi ikirarin cewa, a madadin CTRI, sun kwace ikon shugabancin kasar domin “kawo karshen mulkin da ake akai.” Sanarwar ta zo ne bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta ce an sake zaben Bongo daga jam'iyyar Demokuradiyyar Gabon mai mulki a karo na uku a zaben na ranar Asabar.

Mai Magana da yawun Guterres Stephen Dujarric ya ce, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Laraba ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin na Gabon, kuma yana bibiyar halin da ake ciki a Gabon sosai, yana mai nuna matukar damuwa game da sanar da sakamakon zaben da rahotanni suka bayyana cewa an keta hakkin bil adama.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki a ranar Laraba shi ma ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar Gabon. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Faki ya nuna matukar damuwarsa kan halin da ake ciki a Gabon, ya kuma yi kakkausar suka ga yunkurin juyin mulkin a matsayin hanyar magance rikicin da ya biyo bayan zaben kasar. (Yahaya)