Sin na nuna bakin ciki game da kudurin kakabawa Mali takunkumi da wasu mambobin kwamitin sulhun MDD suka yi
2023-08-31 20:06:19 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin kasar Sin dake MDD Dai Bin, ya yi tsokaci bayan kwamitin sulhun MDD ya jefa kuri’u game da kudurin tsawaita lokacin kakabawa Mali takunkumi, inda ya bayyana matukar bakin ciki game da shawarar da wasu mambobin suka yanke kan aiwatar da kudurin.
Ya ce, kakabawa takunkumi wani mataki ne da aka dauka, ba wai buri ne da aka sa a gaba ba. Kuma bai kamata kwamitin ya ykakabawa wata kasa takunkumi na tsawon lokaci ba, don haka dole ne a yiwa kasar bincike bisa halin da take ciki a halin yanzu, domin gyara ko soke shi.
Jami’in ya ce Sin za ta ci gaba da goyon bayan Mali, wajen kiyaye ikon mulkinta, da cikakken yankinta, da tsaron kasar, da kuma taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiyar kasar ta hanyoyi daban-daban, bisa hadin kai da Mali. (Amina Xu)