logo

HAUSA

An sake zaben Ali Bongo a matsayin shugaban Gabon

2023-08-30 13:47:47 CMG Hausa

 

Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar a yau Laraba cewa, an sake zaben shugaban kasar mai ci Ali Bongo a wa'adi na uku na shugaban kasa a zaben da aka gudanar ranar Asabar da kaso 64.27.

Jim kadan bayan haka, kafafen yada labarai na kasashen waje suka ruwaito cewa, wasu jami’an sojan kasar Gabon sun sanar ta gidan talabijin din kasar na soke zaben da kuma rusa hukumar zaben kasar, suna masu cewa sun kwace mulki.

Rahotanni sun ce, an rufe iyakokin kasar Gabon har sai illa masha Allah. Haka kuma, an ji karar harbe-harbe a Libreville, babban birnin kasar. (Ibrahim)