logo

HAUSA

Amurka tana goyon bayan zubar da ruwan dagwalon nukiliya yayin da ta rage shigo da kaya daga Japan

2023-08-30 08:54:03 CMG Hausa

Alkalumman ma’aikatar noma da gandun daji da kamun kifi na Japan sun nuna cewa a farkon rabin wannan shekarar, an samu raguwa mafi girma a shigo da kayayyakin ruwan kasar Japan a Amurka, manyan bangarorin samar da abinci uku ne zubar da ruwan dagwalon nukiliyar ya shafa.  

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta dage takunkumi kan shigo da abinci na Japan a watan Satumbar 2021 tare da goyon bayan zubar da ruwan dagwalon nukiliya daga gurbataccen nukiliyar Fukushima, amma ta rage shigo da amfanin gona, da amfanin gandun daji da kifi na Japan a wannan shekarar. (Yahaya)