logo

HAUSA

Masanin aikin noma Wang Xuemin: Fasahar aikin noma ta kawo alheri ga al’ummar kasashen Afirka

2023-08-30 10:17:45 CMG Hausa

A karkashin sha’warar “Ziri daya da hanya daya”, an karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya a fannin aikin noma, inda masanan kasar Sin a fannin aikin noma suka ziyarci Nijeriya, don ba da babbar gudummawa kan yadda za a bunkasa aikin noma a Nijeriya.kuma malam Wang Xuemin yana daya daga cikinsu. A watan Oktoba na shekarar 2003, a matsayinsa na kwararre a fannin aikin noma, an tura malam Wang zuwa Nijeriya, inda ya shafe kusan shekaru 20 yana wannan aiki.A cikin shirin mu na yau, za mu kawo muku labarin malam Wang Xuemin.