Ya dace kasashen Sin da Afirka su nemi zamanantarwa cikin hadin gwiwa
2023-08-30 08:00:04 CMG Hausa
Kasar Sin tana yin tattaki zuwa ga burin sabon karni na gina kanta, ta zama babbar kasa mai bin tsarin gurguzu na zamani daga dukkan fannoni masu wadata, da karfi, da dimokuradiyya, da ci gaban al'adu, da jituwa da kuma kyau. Tana kokarin sake farfado da al'ummar kasar daga dukkan bangarori ta hanyar zamanintarwa. Afirka a nata bangaren, tana tafiya cikin sauri zuwa ga kyakkyawan fatan da aka sanya a gaba a nan ajandar 2063, tare da yin dukkan kokarin gina sabuwar Afirka mai cike da zaman lafiya, hadin kai, wadata da karfi.
Ga duk al’ummar dake da burin samun ci gaba, ya zama wajibi ta mayar da hankali ga tsara manufofi, wadanda za su taimaka mata cimma burikan da ta sanya gaba, kuma muhimmin jigo a nan shi ne ci gaba da zamanantar da al’amura, ta yadda manufofin ci gaba za su rika tafiya kafada da kafada da halin da ake ciki, na sauye-sauye a matakai daban daban.
Ga al’ummar kasar Sin, zamanantar da kasa na nufin aiwatar da tsare tsaren cimma burin bunkasa kasa, bisa salon gurguzu ta dogaro da kimiyya. Ta haka kasar ke fatan cimma nasarar farfadowa, da samun manyan nasarorin da daukacin al’ummar Sinawa za su ci gajiya.
Karkashin manufar zamanantarwa ta kasar Sin, ana fatan zamanantar da tunanin babbar al’umma, da cimma nasara tare da dukkanin sassa, da bunkasa al’adu da zamantakewa, da samar da yanayin zaman jituwa tsakanin bil adama da sauran halittu dake kewaye da shi, kana da samar da ci gaba cikin lumana.
Hakan ne ma ya sa a kwanakin baya, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron tattaunawa, na jagororin Sin da Afirka, wanda ya jagoranta tare da shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana muhimmancin cimma wannan buri na zamantar da kasa tare da kasashen Afirka, a matsayin su na abokan tafiya, kuma kasashe masu tasowa.
Shugaba Xi ya ce nahiyar Afirka, wuri ne mai cike da damammakin cimma nasara a wannan karni na 21, kuma Sin za ta ci gaba da tsayawa kan manufofin ta na yin aiki tukuru tare da kasashen Afirka, ta yadda za su kai ga karfafa kawance da hadin gwiwa, bisa martaba juna da adalci kamar dai yadda suka shafe shekaru da dama suna yi.
Kaza lika, shugaban na Sin ya jaddada bukatar sassan biyu, da su kara azamar wanzar da alaka mai nagarta, bisa amincewa juna, da karfafa manufofin cimma nasara tare, da zurfafa fahimtar juna, kana su hada karfi da karfe wajen kare adalci, ta yadda za su gina al’umma mai karfi dake da makomar bai daya ga sassan biyu.
Dukkanin wadannan shawarwari da shugaban na Sin ya gabatar, yayin taron na kwanan baya, muna iya lura da cewa, sun yi daidai da buri guda, wato cimma nasarar hadin gwiwar Sin da Afirka, a fannin zamanantarwa daidai da zamanin da muke ciki. (Saminu Hassan, Mohammed Yahaya)