Zargi maras tushe da Japan ta yiwa Sin ba zai wanke mummunan aikin zubar da ruwan dagwalon nukiliya zuwa teku ba
2023-08-30 14:10:00 CMG Hausa
A 'yan kwanakin da suka gabata, yayin da ruwan dagwalon nukiliya daga tashar nukiliyar Fukushima ke ci gaba da kwarara cikin tekun Pasifik, kasashen duniya suna ta yin Allah wadai da gwamnatin Japan. Sai dai a maimakon gyara kuskuren da ya yi, bangaren Japan ya rika nuna yatsa ga kasar Sin. Kafofin yada labaran kasar Japan da dama sun yi ta yayata zargin da ake yi na cewa, kiyayyar Japanawa a kasar Sin na kara zafafa, kuma Sinawa na daukar matakan "tsana" kan kasar Japan. Firaministan Japan Fumio Kishida da wasu 'yan siyasar kasar da dama, sun bukaci kasar Sin da ta soke takunkumin hana shigo da kayayyakin ruwa na Japan, har ma sun yi barazanar daukar matakai kan wannan lamari.
Wannan wani bangare ne na yakin “ra’ayin jama’a” da Japan ta shirya a hankali. A ranar da Japan din ta fara zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, a cewar hukumar watsa labarai ta kasar Japan NHK, ma’aikatar harkokin wajen Japan ta tsara manufar daidaita abin da aka kira “labaran karya”, yawan kudin da ta ware domin aiwatar da manufar ya kai kusan JPY biliyan 70. Idan aka duba rahoton daidaita ruwan dagwalon nukiliya da Japan ta fitar a shekarar 2020, yawan kudin da Japan ta ware wajen daidaita labaran karya, ya fi kasafin kudin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku yawa har sau 20.
Ana iya ganin cewa, bangaren Japan ya zabi zubar da ruwan dagwalon nukiliya zuwa teku don tsimin kudi, amma ya kashe kudi da yawa don kawata shi. An yi nuni da cewa, bangaren Japan yana zargin Sin yana dora wa kasar Sin laifi ne, domin rikitar da ra'ayin jama'a da kuma mayar da kanta a matsayin "wadda aka raunata", ta boye abin da ta yi na gurbata muhalli da kuma illata lafiyar bil Adama, a yunkurin rage zargin da ake yi mata dangane da batun zubar da ruwan dagwalon nukiliya zuwa teku. (Safiyah Ma)