logo

HAUSA

Kudaden shigar cinikayyar manhaja na kasar Sin ya karu da 13.6% a watanni 7 na farkon bana

2023-08-30 16:13:24 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barka da war haka. Wace irin manhaja wato software kuke amfani da ita? Yau na kawo muku wani labari dangane da ci gaban manhajar kasar Sin.

Bayanai da ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar a kwanan baya sun nuna cewa, masana'antun samar da manhajar kwamfuta ko software da fasahar sadarwa na kasar Sin sun ci gaba da inganta daga watan Janairu zuwa Yuli, yayin da kudin shigar cinikayyar manhaja ya kai yuan biliyan 6,457, wanda ya karu da kashi 13.6 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara.

Sannan jimillar ribar da masana'antar kera manhaja ta samu, ta karu ta zuwa yuan biliyan 737.4, wanda ya karu da kashi 13.4 cikin dari kan makamancin lokaci na bara.

A cikin kayayyaki masu amfani da manhaja, kayayyakin masana’antu masu amfani da manhaja sun fi yin fice, wanda ke nuna ci gaban harkokin fasahar zamani da masana'antun suka samu zuwa wani matsayi.