logo

HAUSA

Majalisar Dinkin Duniya ta ware karin kudade don taimakon 'yan Sudan da rikici ya rutsa da su

2023-08-30 11:13:06 CMG Hausa

A yayin da rikicin Sudan ya tilastawa 'yan kasar miliyan 4.5 barin gidajensu, babban jami'in ba da agaji na MDD ya saki dalar Amurka miliyan 20 a jiya Talata domin tallafawa 'yan gudun hijira.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai da bada agajin gaggawa Martin Griffiths ya ce kudaden da aka samu daga asusun bada agajin gaggawa na CERF ne domin taimakawa karuwar masu bukata a Sudan.

Griffiths ya ce, yayin da bukatun jin kai ke kara tabarbarewa a Sudan, kudaden da ake ba su ya ragu matuka, kuma shirin bayar da agajin jin kai na MDD ga Sudan, wanda ke bukatar dala biliyan 2.6, kashi 26 ne kacal ake samu.

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi da shugaban majalisar koli ta kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan mai ziyara, a ranar Talata sun tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sabbin abubuwan da ke faruwa game da rikicin Sudan.

Sisi ya jaddada matsayar Masar na tsayawa tsayin daka da Sudan da kuma goyon bayan tsaronta, zaman lafiyarta, da hadin kai na yankunanta, musamman a cikin mawuyacin halin da ake ciki a halin yanzu, a cewar sanarwar.

A nasa bangaren, Al-Burhan, wanda kuma shi ne babban kwamandan sojojin kasar Sudan, ya gode wa Masar bisa goyon bayan tabbatar da tsaro da zaman lafiyar Sudan a wannan yanayi na tarihi da ta ke ciki, musamman karbar ‘yan gudun hijra na kasar Sudan. (Yahaya)