logo

HAUSA

Ministan Kamaru Ya Aza Harsashin Aikin Samar Da Ruwan Sha Da Kasar Sin Ke Taimakawa

2023-08-30 10:47:24 CMG Hausa

Kwanan baya, ministan ruwa da makamashi na kasar Kamaru  Gaston Eloundou Essomba, ya aza harsashin aikin samar da ruwan sha da kasar Sin ta taimaka, a garin Garoua Boulai dake yankin gabashin kasar.

Kaddamar da aikin, shi ne kashi na biyu na wannan aikin, wanda ke da nufin inganta samar da ruwa da ma samar da shi a birane 9 na kasar dake yankin tsakiyar Afirka. Kuma kamfanin gine-gine na kasar Sin ko CGCOC Group a takaice ne zai gudanar da aikin.

A cewar babban manajan kamfanin kula da ruwa na kasar Kamaru, Blaise Moussa, tasirin kai tsaye na wannan aikin a karshen matakai biyu na aikin, zai shafi samarwa al’ummomi kusan cubic mita dubu 120 na ruwa.

An kaddamar da aikin ne a shekarar 2014, inda aka gudanar da kashin farko na aikin a birane hudu. Yanzu mataki na biyu na aikin, ya shafi garuruwan Garoua-Boulai, da Dschang, da Garoua, da Maroua da Yabassi. (Ibrahim)