Kasar Amurka ta bayar da taimakon soja da darajarsu ta kai dalar Amurka 250 ga Ukraine
2023-08-30 10:35:22 CMG Hausa
A jiya Talata ne Amurka ta sanar da karin tallafin soja ga kasar Ukraine da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 250.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fada a cikin wata sanarwa cewa sabon kunshin ya hada da makami mai linzami na AIM-9M na tsaron sararin sama, alburusai na manyan makamai masu linzami, manyan bindigogi na 155mm da 105mm, da harsasai sama da miliyan 3 na kananan makamai.
Wannan shi ne tallafin soji na 45 na gwamnatin Biden da ke da alaƙa da PDA ga Ukraine tun daga watan Agustan 2021, bisa ga jerin DoD na sabbin makaman da ake kaiwa Ukraine.
Yayin da rikicin ke ci gaba da ta’azzara, ana samun karuwar adawar cikin gida, musamman daga jam’iyyar Republican, kan amfani da kudaden masu biyan haraji na Amurka wajen kara kudaden da ake baiwa Ukraine babu kakkautawa.(Yahaya)