Shugaban Benin da babban jami’in Birtaniya za su gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin
2023-08-29 19:48:59 CMG HAUSA
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sanar a yau Talata cewa, shugaban kasar Benin Patrice Guillaume Athanase Talon, zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin daga ranar 31 ga watan nan zuwa 3 ga watan Satumba, bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Ban da wannan kuma, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaran da aka yi a yau cewa, babban jami’i mai kula da harkokin wajen kasar Birtaniya James Cleverly, shi ma zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin a ranar 30 ga watan nan. (Amina Xu)