logo

HAUSA

’Yan Nijar na ci gaba da yin allawadai da takunkumin kungiyoyin CEDEAO da UEMOA

2023-08-29 09:53:21 CMG Hausa

Ranar 26 ga watan Yuli, ranar 26 ga watan Augustan shekarar 2023 wata guda ke nan da juyin mulki a kasar Nijar, wanda ya janyo tir da allawadai daga kungiyoyin CEDEAO, wato ECOWAS da UEMOA, da kuma sanyawa kasar takunkumi na kudi da na tattalin arziki. ’Yan Nijar na ci gaba da kiraye-kiraye domin janye wadannan takumkumi. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Maman Ada ya turo mana da wannan rahoto.

Hakika fiye da wata guda da hambarar da mulkin Mohamed Bazoum, lamarin da ya janyo tsuke bakin aljihun Nijar daga wadannan hukumomin yammacin Afrika, na zagaya cikin birnin Yamai domin jin ta bakin ’yan kasa kan wannan mataki. Ga abin da suke cewa,

“To nawa ra’ayi, takunkumi wanda CEDEAO ta sanya ko ECOWAS, abu na wanda na nasaru ne. A lokacin mulkin Bare, har shugaban kasa an kashe mana ita ce ke nan, don haka ita ECOWAS ba ta samu dumi ba, ke nan yanzu wannan mulki da yake nasu nan a turawa, ke nan don haka ECOWAS ba ta yi daidai har sun kawo wani coupure suna yanke mana wuta Najeriya, ke nan mu matsayinmu na ’yan kasa mu dauki buri wanda za mu yi wutarmu ta kanmu, Allah ya ba mu arziki wanda muna zuwa mu tsara wutarmu ga iraniun can gare mu, ga man futer ga charbon...eh” 

“Bai yi mini dadi ba gaskiya saboda Allah da Annabi, wannan ya zama rashin adalci game da wannan abin da aka yi, abin da Allah ya riga ya aiko sai a karbe shi da hannu biyu biyu, kuma a yi hakuri, duk wahala akwai karshenta, dadi kuma akwai karshen shi, amma wannan abin da Allah ya riga ya aiko mana, malamai da shugabanni, da kowa da kowa mai jin ciwon Nijar ya tashi ya shiga gaba ya yi addu’a, ka kai kukanka ga ubangaji, Allah ya kawowa kasarmu kwanciyar hankali da zaman lafiya.”

“Shi dan kasa shi ya san mene ne ke damuwarsa, ga kasa, minene ciwon kasarshi tun yau da aka wannan juyin mulki, don a samu a daidaita ne a gyar, ’yan kasa ba su nan gajin dadin kasa. Saboda shi ne aka yi, amma don Union Africaine ta fidda mu wannan cikin taro babu matsala, ’yan kasa ya kamata su tashi su mike tsaye, ko ba da ba ita ba, akwai ci gaba cikin rayuwa, tun da kasashe da yawa da dama haka suka biyo suka fita daga ciki, sun ci nasara cikin tafiyar tasu. Nijar tana da arzikin kanta da kanta da an tsaya aka sarrafa shi kome, zai ci gaba insha Allah yadda ake dubi ake sa rai kuma kome zai daidaita, sun taimake mu ba su taimake mu ba, Allah shi ne dalilin, kuma Allah shi ne dalilin abun kuma shi ke da sakamako, kuma Allah shi zai kama mana mu ci gaba. Abin da muke so ga ’yan kasa shi ne su hakuri su kara rokon Allah da ya kawo mana shugabannin nan, ya sa mana tausayi cikin zukatansu ya sa su daidaita kasa.”

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.