logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a ci gaba da tallafawa Mali bayan janyewar dakarun MINUSMA

2023-08-29 09:26:49 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira da a ci gaba da tallafawa Mali bayan shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD (MINUSMA) daga kasar.

Wakilin na kasar Sin ya ce, shirin siyasa da zaman lafiya na kasar Mali na cikin wani mawuyacin hali, yayin da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ake kira MINUSMA ke shirin janyewa daga kasar.

Dai Bing ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su sanya batun samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Mali da yankin baki daya a gaban komai, da taimakawa kasar wajen tinkarar duk wani kalubale, da kara yin hadin gwiwa mai zurfi tsakanin MDD da kasar Mali a cikin sabon yanayin da ake ciki.

Ya shaidawa kwamitin sulhu cewa, akwai bukatar a ci gaba da ba da goyon baya ga shirin siyasa da zaman lafiya a Mali.(Ibrahim)