logo

HAUSA

Mendo'o:Ina kokarin kara fahimtar kasar Sin

2023-08-29 09:18:52 CMG Hausa

 

Joseph Olivier Mendo'o, dan kasar Kamaru ne da ke karatu a jami’ar Peking ta kasar Sin. Ya taba rubutawa shugaba Xi Jinping na kasar Sin wasiku biyu a shekarar 2021, daya a madadin daliban kasa da kasa da ke karatu a jami’ar Peking dayan kuma a madadin matasan kasa da kasa dake kasar Sin.

A cikin wasikun, ya bayyana ra’ayoyin matasan kasa da kasa kan yadda kasar Sin ta fitar da dukkan jama’arta daga kangin talauci. Shugaba Xi ya amsa wasikun, tare da gayyatar su kai ziyara a sassa daban daban na kasar Sin don kara sanin JKS da kuma kasar Sin. Gani ya kori ji. Kamar yadda shugaba Xi ya ba da shawara, Mendo'o ya ziyarci wasu wuraren kasar Sin don ganewa idonsa ci gaban kasar Sin. (Tasallah Yuan)