Shin Amurka Za Ta Cika Alkawurranta A Wannan Karon?
2023-08-29 19:52:29 CMG HAUSA
DAGA Faeza Mustapha
Ziyarar sakatariyar harkokin cinikayya na Amurka Gina Raimondo a kasar Sin, tana ci gaba da daukar hankalin kafafen yada labarai, inda ake bayyana mabambantan ra’ayoyi.
Tuni dai muka riga mu kan san cewa, Amurka ce ta fara kaddamarwa tare da ci gaba da rura yakin cinikayya tsakaninta da Sin. Sai dai, bisa dukkan alamu kamar yadda aka yi hasashe, ita ce ta fi jin radadin matakan a jikinta. Misali, a cewar sakatariya Gina Raimondo, idan Sin ta koma matakin da take a shekarar 2019 a bangaren yawo bude ido kadai, to hakan zai karawa Amurkar dala biliyan 30 cikin tattalin arzikinta tare da samar da guraben ayyukan yi sama da 50,000.
Da alamu irin dimbin alfanun da kasar Sin za ta kawo mata ne ya sa take son kyautata hulda tsakaninta da Sin musamman ta fuskar cinikayya, ganin yadda ta soke jerin sunayen wasu kamfanonin Sin da a baya ta sanyawa takunkumai, gabanin ziyarar madam Raimondo.
Cikin lokaci mai tsawo, kasar Sin ta jajirce wajen raya kanta tare da zama mai matukar muhimmanci ta fuskar samar da kayayyaki da cinikayya da ma jagorantar bangarorin kere-kere daban-daban, lamarin da ya sanya ta zama wani bangare mai matukar muhimmanci ga kamfanonin kasashen waje, ciki har da na Amurka.
A ganina, yadda kasar Sin ke ci gaba da samun habakar tattalin arziki, da kuma yadda Amurka ke jin radadin illolin matakanta, sun tilastawa Amurka neman kyautata huldarta da kasar Sin, bisa la’akari da yadda jami’anta ke ci gaba da kawo ziyara kasar.
Kamar yadda bangarorin biyu suka bayyana, za su kyautata tuntubar juna a tsakaninsu domin a rika tattaunawa a kai a kai. Ko shakka babu, rashin fahimta na daya daga cikin matsalolin da a kan samu a dangantakar manyan kasashen biyu. Don haka, tuntubar juna zai taka muhimmiyar rawa wajen fahimtar manufofi da dabarun juna.
Duk da cewa Amurka na nuna kudurinta na son kyautata hulda tsakaninta da kasar Sin, ta kan kuma aiwatar da abubuwan da su kan saba da huldar kasa da kasa. Amurka ta fi mayar da hankali ne kan ribar da za ta samu ko da kuwa daya bangaren zai yi asara, yayin da kasar Sin ke neman moriyar juna domin a gudu tare a tsira tare. Shawara dai ya ragewa Amurka, ko ta cika alkawuran da ta dauka da girmama alakarta da Sin, ko ta ci gaba da dandana kudarta. (Faeza Mustapha)