logo

HAUSA

Shugaban Faransa ya umarci jakadan kasarsa a Nijar da kada ya fice daga kasar

2023-08-28 20:11:32 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya gabatar da wani jawabi, wanda a cikin sa ya ce duk da matsin lambar sojojin juyin mulki a janhuriyar Nijar, na bukatar jakadan Faransa dake kasar da ya fice ba tare da bata lokaci ba, a nasa bangare shugaba Macron, na umartar jakadan kasar ta sa Sylvain Itte, da ya ci gaba da kasancewa a Nijar, tare da gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata.

Tun a ranar Juma’ar makon jiya ne dai ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwa ta janhuriyar Nijar, karkashin gwamnatin soji dake mulkin kasar, ta fitar da wata sanarwa, wadda cikin ta aka umarci jakadan Faransa dake kasar Sylvain Itte, da ya fice daga kasar cikin sa’o’i 48. (Saminu Alhassan)