logo

HAUSA

Song Yin: Mace ta farko da ta dukufa wajen ceton rayuka a lokutan ba da agajin gaggawa a kasar Sin

2023-08-28 14:47:23 CMG Hausa


Song Yin jagaba ce, wadda Kyaftin ce ta kungiyar farko ta jiragen sama masu ayyukan ceto ta Donghai, a karkashin ma'aikatar sufuri ta kasar Sin. Kana tana daya daga cikin kyaftin mata na farko matuƙan jirgin sama mai saukar ungulu na aikin bincike da ceto a kasar. Tuni Song ta tabbatar da cancantarta, bisa yadda ta kashe sa'o'i sama da 3,395 wajen tukin jirgin sama, ciki har da sa'o'i 1,085 na tukin jirgi don aikin ceto, a cikin shekaru 15 da suka gabata. Bugu da kari kuma, a wannan lokacin, Song ta gudanar da ayyukan ceto 318, kuma ta taimaka wajen ceto mutane 225 a teku. Domin jajircewarta da azama, ake kiran ta da "Kyaftin Mace Mafi Kyau A Kasar Sin".

A cikin shekarar 2021, an kafa dakin kirkira na Song Yin. Song da tawagarta sun kirkiro hanyoyinsu don gudanar da ayyuka cikin inganci. Alal misali, wata rana, a cikin Nuwamba na shekarar 2021, wani mutum ya ji rauni a idanunsa yayin da yake aiki a cikin jirgin ruwa. Don bada agaji cikin sauri, da kuma tabbatar da cewa mutumin ya samu kulawar da ta dace, Song ta tashi jirgin sama mai saukar ungulu kai tsaye zuwa asibitin Shanghai Ruijin bayan da aka ceto mutumin, maimakon kai mutumin asibiti a motar daukar marasa lafiya. Gaba dayan aikin ya dauki kasa da awa daya.

"Ka baiwa mutane daman su rayu, kuma ka bar wa kanka hadarin mutuwa." Wannan ita ce akidar Song da mambobinta. Ko da yake kowane ceto a teku yana da hadari, Song ba ta tsorata ba. Ta ce, "A cikin kowane aiki, ko da yaushe ina natsuwa kuma ina mai da hankali sosai. Wannan ita ce kwarewar da ya kamata muke da ita, kuma shi ne babban nauyin da aka sauke a wuyanmu".

Idan tana magana game da sana'arta da 'yan uwa da abokan arziki, Song sau da yawa ta kan ce kasancewarta matukiyar jirgi mai bincike da ceto shi ne mafi kyawun aiki a gare ta, kuma ceton rayuka shi ne burinta.

A matsayinta na kyaftin, Song ta yi iya kokarinta ganin wadanda ke cikin hadari ba su yanke kauna da rayuwa ba. Ko da yake aikin sau da yawa yana cike da kasada da wahalhalu, Song ko yaushe tana yiwa rayuwa kyakkyawar kauna, kuma ko yaushe akwai murmushi a fuskarta.

Tana da sha'awar abubuwa masu yawa, kamar gudu, hawan dutse, daukar hoto, da wasan ƙwallon kwando. Song ta kuma sanya hotuna da gajerun bidiyo na shirye-shiryenta na horarwa a dandalin sada zumunta, irin su Weibo da Bilibili, don taimakawa mutane su fahimci sana'arta.  Kyakkyawar kuzarinta, lafiyar jikinta da kwarjininta sun sa mutane da yawa, musamman ma masu amfani da yanar gizo, suna kiranta da "Kyaftin Mace Mafi Kyau A Kasar Sin".

Wasu lokuta, mutane suna mamakin dalilin da ya sa mata ke shiga irin wannan aiki mai matukar hadari da jan hankali. Song ta ce an sha yi mata wannan tambayar. "Ina ganin babu wani bambanci tsakanin maza da mata wajen tukin jirgin ceto. Abin da ke da muhimmanci kawai shi ne cikakken ingancin kwarewar matukin. Kasancewa mace ba wani shamaki ba ne ko gata", in ji ta.

Song ta kara da cewa, "fiye da shekaru 50 da suka wuce, NASA tana da fitattun mata bakaken fata guda uku, wadanda suka ba da gudummawar da ba za a iya maye gurbinsu ba a masana'antar sararin samaniya ta Amurka ba. Ba su taba yin kasa a gwiwa ba wajen fuskantar shakku da rashin adalci, an yi wani fim mai suna “Hidden figure” wato “boyayyun mutane” da labarinsu. Mun fi su sa'a, yayin da muke rayuwa a cikin wani zamani na wayewar kai, da kuma muhalli mafi daidaito. Na yi sa'ar samun damar yin aiki a matsayin kyaftin, kuma ina godiya ga mambobin tawagata saboda goyon bayan da suka ba ni".  

Bayan kowane nasarar ceto, akwai horo mai wahala kowace rana. Daga tukin jirgi da rana zuwa tukin jirgi da daddare, Song ta ci gaba da inganta fasaharta, ta hanyar shirye-shiryen horarwa masu wahala, kuma ta ƙara fahimtar rayuwa. Ta ce, "Mun fifita ceto rayukan mutane, amma sadaukar da rai don ceton wani rai ba shi ne abin da muke so ba. Ina fatan baiwa mutane dama da kwanciyar hankali ta hanyar kwarewa ta".

A shekarar 2012, Song ta halarci taron bincike da ceto na Turai a kasar Ireland, inda ta gabatar da jawabi kan dabarun bincike da ceto, da fasahohin kasar Sin, da shirin raya kasa. Ta kuma ziyarci kwalejoji da jami'o'i, inda ta ba da labarin abubuwan da ta samu a matsayin kyaftin da fatan karfafawa matasa gwiwa su zama ma'aikatan jirgin sama masu bincike da ceto.

Mace kwararriyar matukiyar jirgi a cikin fim mai suna The Rescue da aka nuna a shekarar 2020, labarin a kan Song Yin ne. "Kalubalen na farawa ne daidai lokacin da jirgin sama mai saukar ungulu dake aikin bincike da ceto ta tashi. Ga mambobin tawagarmu na jirgin sama na ceto, ko wace manufa na nufin tseranya da lokaci. Manufarmu ita ce mu sa ayyukan ceto su kasance mafi aminci da inganci. Za mu ci gaba da yin aiki tukuru. kuma mu ci gaba da inganta basirarmu", in ji Song.

A shekarar 2022, Song ta samu lambar yabo ta ma’aikata mafiya nagarta ta ƙasar Sin saboda jajircewarta na ceton rayuka a lokutan ba da agajin gaggawa. A cikin watan Maris din shekarar 2023, kungiyar mata ta kasar Sin ta nada Song Yin a matsayin mace mafi nagarta ta kasar Sin, kuma sashen wayar da kan jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta ƙasar Sin da kungiyar mata ta kasar sun nada ta a matsayin mace mafi kyawu cikin mata masu gwagwarmaya. Song Yin ta bayyana cewa, "Wadannan karramawa suna dada karfafa min gwiwa. Abin da ya wuce shi ne gabatarwa. Da kuma mafari, zan ci gaba da bin burina, da kuma ci gaba a kan sabuwar tafiya". (Kande Gao)