logo

HAUSA

Kasashen Masar da Habasha da Sudan sun koma tattaunawa kan rikicin madatsar ruwan Nilu

2023-08-28 10:06:43 CMG Hausa

Ma’aikatar albarkatun ruwa da aikin ban ruwa ta kasar Masar ta bayyana cewa, an fara wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin kasashen Masar da Habasha da Sudan a birnin Alkahira na kasar Masar, kan takaddamar da aka dade ana yi dangane da babbar madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam wao (GERD) a takaice.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar jiya, ta bayyana cewa, ministan albarkatun ruwa da aikin ban ruwa na Masar Hani Sewilam ya jaddada wajabcin cimma matsaya ta doka kan dokokin cikewa da sarrafa madatsar ruwar da aka gina a yankin kogin Nilu na kasar Habasha, yana mai cewa, ya kamata yarjejeniyar ta yi la'akari da muradu da damuwar kasashen uku.

Bayan shafe tsawon shekaru ana tattaunawa ba tare da cimma wata matsaya ba, kasashen biyu wato Masar da Sudan na fatan cimma matsaya ta doka tare da kasar Habasha da ke kula da alhakin kula da batun cikawa da gudanar da ayyukan madatsar ruwar ta GERD.(Ibrahim)