logo

HAUSA

Hukumomin Rasha sun tabbatar da mutuwar shugaban Wagner a hatsarin jirgin sama

2023-08-28 09:58:41 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne kwamitin binciken kasar Rasha ya tabbatar da mutuwar shugaba Yevgeny Prigozhin a wani hatsarin jirgin sama a yankin Tver da ke kusa da birnin Moscow.

Kwamitin ya kara da cewa, sakamakon binciken bayanan dukkan mutane 10 da suka mutu a hatsarin ya yi daidai da bayanan fasinjojin jirgin. 

A ranar Larabar ne wani jirgin sama kirar Embraer mai zaman kansa da ke kan hanyarsa daga Moscow zuwa St. Petersburg ya fadi a yankin Tver, inda dukkan mutane 10 da ke cikin jirgin suka mutu, a cewar ma’aikatar ayyukan gaggawar kasar. (Mohammed Yahaya)