logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren ta game da matsayin dakarun sojin kasar

2023-08-27 15:19:44 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan, ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren ta, game da ayyana dakarun sojin kasar a matsayin masu rura wutar yaki.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya Asabar, ta ce bai kamata Amurka ta yiwa dakarun sojin kasa, da sojojin ko ta kwana na SAF kudin goro, wajen bayyana su a matsayin sojoji masu aikata ta’addanci ba.

Sanarwar ta soki lamirin wani sako ta shafin sada zumunta da jakadan Amurka a Khartoum John Godfrey ya wallafa, wanda a cikin sa ya kira sassan biyu dake dauki ba dadi a Sudan, wato rundunar SAF da ta RSF, a matsayin masu aikata laifin yaki, tare da cewa dukkanin su ba su cancanci jagorantar kasar ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan, ta bukaci jakada Godfrey da gwamnatin Amurka, su gyara kuskuren su, su kuma sauka daga wannan matsayi na rashin adalci. A hannu guda sanarwar ta bukaci jakadan na Amurka, da ya kaucewa furta kalaman da suka sabawa ka’idojin diflomasiyya, wadanda ba za su taimaka wajen warware rikicin na Sudan ba.  (Saminu Alhassan)