logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Kasashen Duniya Da Su Dauki Matakin Dakatar Da Japan Daga Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku

2023-08-26 15:44:10 CMG Hausa

A jiya ne, kasar Sin ta yi kira ga daukacin kasashen duniya da su hada kai, wajen yin kira ga kasar Japan da ta dakatar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya daga tashar nukiliyar Fukushima Daiichi zuwa cikin teku.

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya shaidawa babban zauren MDD cewa, wajibi ne a kaucewa haifar da illa da hadari ga muhallin teku na duniya da lafiya da jin dadin al’ummar duniya.(Ibrahim)