logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Niger ta bullo da tsarin hutun watanni 6 ga mata ma’aikata domin shayar da jariran da suka haifa

2023-08-26 14:58:13 CMG Hausa

A wani mataki na karfafa tsarin shayar da jarirai nonon uwa, gwamnatin jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta zartar da shawarar bayar da hutun watanni 6 ga mata ma’aikata da suka haihu.

Babban sakatariya a hukumar tsare-tsare ta jihar Niger Hajiya Ramatu Umar ce ta tabbatar da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka tattauna kan batun, haka kuma tsarin ya hada biyan ma’aikatan albashinsu a tsawon lokacin hutun.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babbar sakatariyar ta ce, tsarin da ake bi a baya na mata su rinka dawowa bakin aiki kafin cikar watanni 6 bayan haihuwa, yana shafar koshin lafiyar jarirai da su kansu  iyaye, saboda abu ne mai wahala mace ta iya hada aiki da shayarwa a lokaci guda.

“Batun shayar da nonon uwa yana da muhimmanci ga rayuwa. Yana kara inganta lafiyar iyaye mata da jarirai sannan yana kara kwazon yara da tsawon rayuwa mai amfani.”

A lokacin da take jawabi, kwararriyar likita a bangaren sha’anin abinci mai gina jiki Hajiya Amina Isa ta ce, daukar lokaci wajen shayar da jarirai wadataccen nonon uwa yana taimakawa sosai wajen samar da tazarar iyali, sannan yana rage karuwar yawan al’umma. A saboda haka ta ce, akwai matukar bukatar gwamnatoci su bayar da dukkan taimakon da ya kamata ga mata masu shayarwa da kuma masu kula da yara wadanda suke cikin aikin gwamnati da masu aikin wucin gadi.

“A watanni 6 na farkon haihuwa ana bukatar mai jego ta shayar da jaririn ta zalla nono ba tare da ba shi ruwa ba, amma kuma bayan watanni shidan za ta ci gaba da shayar da shi tare kuma da ba shi sauran abinci.” (Garba Abdullahi Bagwai)