logo

HAUSA

Sin da Afirka abokan tafiya ne wajen cimma burin zamanintar da kasa

2023-08-25 21:08:36 CMG Hausa

A bana ake cika shekaru 10 da aiwatar da manufofin Sin kan nahiyar Afirka na nuna gaskiya da sahihanci da hadin kai da kuma adalci. A cikin shekaru 10 da suka gabatar, an aiwatar da ayyuka da dama a tsakaninsu, kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cikin jawabinsa a gun taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afirka a jiya cewa, Sin tana son yin hadin gwiwa tare da Afirka wajen cimma burin zamanintar da kasa.

A halin yanzu, kasar Sin tana zamanintar da kanta daga dukkan fannoni bisa salon musamman na kasar, kuma tana maraba da kasashen Afirka da su samu damar ci gaba. Sin tana goyon bayan kokarin da kasashen Afirka ke yi wajen zamanintar da kasa da kuma samun bunkasuwa da kansu. A gun taron tattaunawar na wannan karo, shawarar goyon bayan raya masana’antun Afirka, shirin taimakawa Afirka wajen zamanintar da aikin gona, da kuma shirin horar da kwararrun Sin da Afirka daa shugaba Xi Jinping ya gabatar, sun biya bukatun Afirka na zamanintar da kansu, da sa kaimi ga Afirka wajen inganta karfinsu na samun bunkasuwa da kansu, da kara azama kan dunkulewar Afirka, da kuma kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka.

Yayin da ake kokarin zamanintar da kasa, Sin tana son yin kokari tare da Afirka wajen neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, da kuma samarwa jama’arsu kyakkyawar makoma. (Zainab)