logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun bayyana damuwarsu kan matakan tilastawa na gashin kai

2023-08-25 00:25:44 CMG HAUSA

 

A ranar Alhamis ne kasashen BRICS suka bayyana damuwarsu kan yadda ake amfani da matakan tilastawa na gashin kai, wadanda ba su dace da ka'idojin kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma suna haifar da mummunar illa kan kasashe masu tasowa.

A cikin sanarwar Johannesburg na biyu da aka amince da ita biyo bayan taron kolin BRICS karo na 15 na kwanaki uku, kasashen BRICS sun kuma nanata kudurinsu na inganta da kyautata gudanar harkokin kasa da kasa, sa kaimi kan raya tsarin sassa daban daban na duniya mai dacewa, inganci, wakilci, da dimokiradiyya. (Yahaya)