logo

HAUSA

Za a kara bullo da hanyoyin karfafa ilimin yara masu bukata ta musamman a jihar Kaduna

2023-08-25 09:17:43 CMG Hausa

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna ta tabbatar da aniyarta ta shigo da yara masu bukata ta musamman cikin shirye-shiryenta na tallafin ilimi tun daga tushe domin ganin cewa sun kasance masu bayar da gudummawa ga dukkan fannonin ci gaban kasar.

Babbar jami’ar mai lura da sashen fadada tallafin ilimi ga yara na hukumar ilimi ta  karamar hukumar Jema’a Mrs Josephine Paul Ekpo ce ta tabbatar da hakan lokacin da ta ziyarci wata cibiyar bayar da horon jarrabawar shiga sabbin aji wanda aka shiryawa wasu yara masu bukata ta musamman a yankin karamar hukumar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Madam Josephine Paul ta ce, sau tari dai gwamnatoci da wasu kungiyoyin bada tallafin ilimi na kasa da kasa da suke Najeriya su kan fi mayar da hankali ne ga ilimin yaran da suke da koshin lafiya, ba tare da la’akari da sauran yara da suka gamu da wata matsala a fannin lafiyar jiki ba.

Ta ce, a sakamakon hakan ne gwamnatin jihar ta Kaduna ta hannun hukumomin ilimi na kananan hukumomin jihar ta bijiro da tsarin tallafawa ilimi irin wadannan yara, domin dai ana samun masu kaifin basira a cikinsu da gwamnati da al’ummar za su iya amfana.

Babbar jami’ar wadda ta yaba da yadda shirin ke tafiya cikin nasara a karamar hukumar ta Jema`a, inda ta ce gibin dake tsakanin yara da suke da lafiya da masu bukata ta musamman ta bangaren ilimin firamare da sakandire a yankin ba shi da yawa sosai, wanda wannan shi ne burin da gwamnatin jihar ta Kaduna ke son cimmawa.

Sai dai ta koka ainun kan yadda wasu iyaye ke kin barin ’ya’yansu zuwa makarantun duk da cewa gwamnati  ce ke daukar dawainiyarsu, inda ta yi kira ga irin wadannan iyaye kamar haka, 

“Don haka ku fito da su duk inda kuka boye su, ni Madam Josephine ina nan shirye idan na ji makarantar da kuka kai ba su karbe su ba, ku gaya mini, don haka ina kara cewa ku fito da su, su zo su yi karatu domin su zama na-gari gobe, an ce na-gari na kowa mugu sai mai shi, akwai horewa cikin ganin rashi wato akwai ability cikin disability.”

Yaran da suka samu halartar jarrabawar gwajin da kuma na canjin aji sun hada da guragu, makafi da kurame. (Garba Abdullahi Bagwai)