logo

HAUSA

Yaya za a samu bunkasuwa mai inganci bayan da aka shigar da sabbin membobi cikin tsarin BRICS?

2023-08-25 00:11:31 CMG Hausa

A safiyar jiya Alhamis 24 ga wata, an gudanar da taron manema labaru na musamman na taron kolin BRICS karo na 15 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, inda aka sanar da cewa, an gayyaci Saudiyya, Masar, Hadaddiyar daular Larabawa, Argentina, Iran, da Habasha don zama membobin tsarin BRICS a hukumance.

Wannan ne daya daga cikin manyan nasarorin da aka samu a gun taron kolin BRICS a wannan karo, wanda ya shaida imanin BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, China da South Africa kan yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa. A matsayin kasashe masu wakiltar kasashen da suka fi samun ci gaban kasuwanni a duniya, kasashen BRICS sun yi kokari wajen raya dangantakar abokantaka mai inganci. Yaya za a raya wannan dangantakar? Sin ta bayar da shawarwari.

Sin ta gabatar da shawarar kafa yankin yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha a tsakanin Sin da kasashen BRICS don sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci tare. Kiyaye tsaro shi ne tushen samun bunkasuwa. Sin ta gabatar da shawarar fadada hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS a fannonin siyasa da kiyaye tsaro, wannan ya shaida bukatun dukkan mutane masu neman zaman lafiya a duniya. Hakazalika kuma, an yi hadin gwiwa mai inganci a tsakanin kasashen BRICS, ta hakan za a daga muryar kasashe masu tasowa wajen samun damar fada a ji a duniya. (Zainab)