Kasar Sin ta bukaci a sa kaimi ga yunkurin samun tsagaita bude wuta a rikicin Rasha da Ukraine
2023-08-25 11:07:41 CMG Hausa
Zaunannen Wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD kan batun Ukraine a jiya 24 ga wata cewa, dole ne a yi kokari don sa kaimi ga yunkurin samun tsagaita bude wuta da dakatar da rikici tsakanin Rasha da Ukraine, gami da kokarin shawo kan tasirin rikicin kan sauran yankuna.
Zhang Jun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin ta nanata cewa, ya kamata a kare ikon mulkin kai da na tabbatar da cikakken yankin kasa, da mutunta manufofi da ka'idojin MDD, kuma a mayar da hankali kan damuwar bangarori daban daban game da batun tsaro, kana kamata ya yi a goyi bayan duk wani yunkuri na warware rikici cikin lumana. Bisa wannan matsaya da ta dauka, kasar Sin tana ta kokarin neman ganin a dawo da zaman lafiya a inda ake samun abkuwar rikici.
Jami’in ya ce, ya kamata manyan kasashe masu sukuni su dauki matakan da suka dace na tattalin arziki da kasuwanci don tabbatar da tsaro, da daidaita tsarin masana'antu da na samar da kayayyaki a duniya, kuma a daina kakaba takunkumi maras dacewa daga gefe daya kurum, sannan a daina siyasantar da batun tattalin arziki da mayar da shi makami don neman biyan bukata. Bai kamata a yi watsi da yarjejeniyar fitar da kayayyakin amfanin gona daga tashoshin jiragen ruwa dake cikin Bahar Aswad cikin sauki ba. Kasar Sin na fatan bangarori daban daban masu ruwa da tsaki za su yi kokarin maido da aikin fitar da hatsi da taki daga kasashen Rasha da Ukraine tun da wuri, ta hanyar tattaunawa da shawarwari. (Mai fassara: Bilkisu Xin)