logo

HAUSA

Juyin mulkin Nijar ya kawo cikas wajen janye sojojin Majalisar Dinkin Duniya daga Mali

2023-08-25 09:46:59 CMG Hausa

Mai magana da yawun MDD a jiya Alhamis ta ce, dagulewar yanayi a Nijar ya kawo cikas ga janyewar dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD daga makwabciyarta Mali.

Florencia Soto Nino, mataimakiyar mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ta ce, abubuwan dake faruwa a yanzu a yankin suna kara rikirkita aikin da dama mai rikitarwa ne. Kuma tsarin lokaci ya yi kadan, "Don haka, muna duba yadda juyin mulkin zai iya shafar ayyukan janye dakarun," a cewarta.

A watan Yuni ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yanke shawarar dakatar da wa’adin aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali (MINUSMA) tare da ba da wa’adin watanni shida har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023 don kammala janyewar. (Muhammed Yahaya)