logo

HAUSA

Sin ta bukaci Japan da ta dakatar da zubar da gurbataccen ruwan nukiliyar Fukushima a cikin teku

2023-08-24 15:56:13 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na adawa da kuma yin tir da matakin Japan na sakin gurbataccen ruwan nukiliya na Fukushima a cikin teku, inda ta bukaci gwamnatin kasar Japan da ta dakatar da wannan danyen aiki.

A yau ne, ba tare da la’akari da kakkausar suka da adawar da kasashen duniya ke yi ba, gwamnatin Japan ta yi gaban kanta ta fara sakin gurbataccen ruwan tashar nukiliyar Fukushima a cikin teku.

Sanarwar da kakakin ya fitar, ta bayyana cewa, kasar Sin tana adawa matuka da wannan lamari, da ma yin Allah wadai da shi.

A sa'i daya kuma, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sanarwa, inda ta yanke shawarar dakatar da shigo da kayayyakin ruwa da suka fito daga kasar Japan, tun daga ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2023. (Ibrahim Yaya)