logo

HAUSA

Kumbon binciken duniyar wata na Indiya ya sauka cikin nasara

2023-08-24 12:02:58 CMG Hausa

A yammacin jiya Laraba misalin karfe 6 da mintuna 4, agogon kasar Indiya, kumbon binciken duniyar wata na kasar mai lakabin Mission-3, ko “Chandrayaan-3, ya sauka a doron wata cikin nasara.

A cewar hukumar binciken samaniya ta kasar ISRO, Indiya ta zamo kasa ta 4 a duniya, cikin jerin kasashen da suka yi nasarar sauka a duniyar wata, baya ga tsohuwar tarayyar Soviet, da Amurka da Sin. (Saminu Alhassan)