logo

HAUSA

Tsarin BRICS Ya Zama Dandalin Kare Moriyar Kasashe Masu Tasowa

2023-08-24 23:12:10 CMG Hausa

Taron kolin BRICS da ya gudana a kasar Afrika ta Kudu a kwanakin nan ya gabatar da wasu salon musamman na Afirka. Da farko, kasar Afrika ta Kudu ce ta dauki nauyin karbar bakuncin taron. Na biyu, cikin manyan kusoshi fiye da 60 da aka gayyata don halartar taron, a kalla akwai manyan jami’ai 30 wadanda suka zo daga kasashen Afirka. Na uku, cikin kasashe 6 da aka gayyace su don su zama mambobin tsarin BRICS a wannan karo, akwai wasu kasashe 2 dake cikin nahiyar Afirka, wato Masar, da Habasha.

Ban yi mamaki ba kan yadda taron BRICS ya nuna yanayi mai alaka da nahiyar Afirka, saboda nahiyar ta kunshi mafi yawan kasashe masu tasowa. Yayin da tsarin hadin gwiwa na BRICS ya riga ya zama wani muhimmin dandali ga kasashe masu tasowa, don su karfafa hadin gwiwa, tare da kare moriyarsu ta bai daya.

Me ya sa ake bukatar wani nau’in dandali kamar haka? Saboda yayin da tattalin arzikin duniya ke fama da yanayi na koma baya, kana rikice-rikice na ci gaba da kasancewa a wasu yankuna, tsare-tsaren kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da siyasa da kasashen yamma ke jagoranta, na kara karkata ga moriyar kasashen yamma ne, maimakon ba da kulawa ga kasashe masu tasowa.

Alal misali, da yawa daga cikin shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, matsayin dalar Amurka mai muhimmanci ya hana tattalin arzikin kasashensu ci gaba. Saboda yadda kasar Amurka ke kara kudin ruwan ajiya a kai a kai ya haddasa hauhawar darajar kudin kasar, wanda ke sanya sauran kasashe kashe kudi fiye da kima don shigar da kayayyaki daga ketare, gami da karuwar yawan basusukan da ake binsu. Game da matsalolin da karuwar darajar dalar Amurka ke haddasa wa tattalin arzikin sauran kasashe, na san abokanmu dake Najeriya sun fahimce su sosai.

Sa’an nan a fannin harkar siyasar kasa da kasa, kasar Amurka da kawayenta na yammacin duniya sun sa hannu cikin rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine, inda suke ba da taimako ga wani bangare, gami da tilastawa sauran kasashe bin sahunsu. Sai dai kasashen Afirka suna son ci gaba da hadin gwiwa da kasar Rasha, da neman ganin an kawo karshen yakin da ake yi cikin sauri, kuma ta hanyar lumana, bisa la’akari da moriya kansu.

A sa’i daya, kasashen Afirka da kasashe masu tasowa na sauran yankuna suna son ganin gyare-gyare kan tsare-tsaren bankin duniya, da hukumar ba da lamuni ta duniya, da kasashen yamma suka kafa, don magance samar da karin tallafi ga kasashe masu sukuni, maimakon kula da kasashe marasa karfi. Wadannan abubuwan da na ambata suna cikin cece-kuce da ake samu tsakanin kasashe masu tasowa, da kasashen yamma, sakamakon bambancin moriyar su.

Saboda haka, yadda tsarin BRICS yake habaka, da yadda yake sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin hada-hadar kudi na duniya, sun yi daidai da bukatun dimbin kasashe masu tasowa. Inda a ganinsu, ci gaban da tsarin BRICS ya samu ya nuna yadda kasashe masu tasowa ke samun karin ikon fada a ji a duniya, da karin damammaki na tabbatar da moriyarsu. Batun nan ya yi kama da maganar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada a wajen taron kolin BRICS na wannan karo, inda ya ce, ya kamata kasashen BRICS su haifar da sauyin yanayi ga tsarin kula da duniya, don neman tabbatar da adalci da kima, da wani yanayi na tabbas, da karko, gami da ci gaba.

Idan karin kasashe masu tasowa sun karfafa hadin gwiwarsu ta hanyar tsarin BRICS, to, za su samu isashen karfin yin garambawul kan tsare-tsaren duniya. Saboda ko kasashe mambobi guda 5 da suke cikin tsarin a halin yanzu, wato Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin, da Afirka ta Kudu, sun riga sun dauki kaso 24.3 na tattalin arzikin duniya, da kaso 26.46 na fadin harabar kasashen duniya, gami da kaso 43 na daukacin al’ummar duniya. Yayin da ake sa ran ganin karuwar wadannan adadi a kai a kai a nan gaba. (Bello Wang)