logo

HAUSA

Wasu manyan kusoshin kamfanin Wagner sun rasu sakamakon hadarin jirgin sama

2023-08-24 08:57:55 CMG Hausa

Hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Rasha, a jiya Laraba ta gabatar da jerin sunayen mutanen da suka rasu sakamakon hadarin jirgin sama da ya auku a jihar Tver ta kasar, inda ta gaskata cewa, mutumin da ya kafa kamfanin sojojin haya mai zaman kansa wato Wagner, mista Yevgeny Prigozhin, da kuma kwamandan dakarun na Wagner Dmitry Utkin sun rasu a wannan hadari.

Kana, bisa jerin sunayen da hukumar ta fitar, an ce akwai fasinjoji 7 dake cikin jirgin saman, wadanda suka hada da kusan dukkanin manyan shugabannin kamfanin na Wagner. (Maryam)