logo

HAUSA

Ministan wajen Aljeriya ya fara ziyara a kasashen yammacin Afirka da nufin shawo kan rikicin Nijar

2023-08-24 13:57:52 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya, da harkokin al’ummun kasar mazauna waje Ahmed Attaf, ya fara ziyara a wasu kasashen yammacin Afirka, da nufin shawo kan batun juyin mulkin Nijar dake haifar da takaddama.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta fita, ta ce a jiya Laraba ne Ahmed Attaf ya fara ziyarar ta sa, inda ake sa ran zai gana da jami’ai a kasashen Najeriya, da Benin, da Ghana, a wani yunkuri na shawo kan rikicin kasar ta Nijar.

Kaza lika, sanarwar ta ce Attaf zai tattauna da takwarorin sa na kasashen yammacin Afirka, mambobin kungiyar ECOWAS, game da zakulo hanyoyin kawo karshen takaddamar ta Nijar, tare da kandagarkin ci gaba da tabarbarewar yanayin da ake ciki.

Ana sa ran mista Attaf, zai maida hankali ga lalubo hanyoyin sulhu na siyasa, wadanda za su kare janhuriyar Nijar, da ma yankin baki daya daga fadawa tashin hankali, sakamakon yanayin da ake ciki yanzu na kika-kaka. (Saminu Alhassan)