logo

HAUSA

Akwai Fata Mai Kyau A Dangantakar Sin Da Afirka Ta Kudu

2023-08-23 21:25:30 CMG Hausa

A bana ne aka cika shekaru 25 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. Ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping ya kai Afirka ta Kudu a wannan karo, ita ce ta hudu da ya ziyarci Afirka ta Kudu a matsayinsa na shugaban kasar Sin. A jiya Talata, yayin da shugabannin kasashen biyu suka yi shawarwari, sun amince da yin hadin gwiwa tare da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka ta Kudu zuwa wani sabon matsayi, da gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka ta Kudu.

Afirka ta Kudu ita ce kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta shiga hadin gwiwar aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya", kuma ta zama babbar abokiyar cinikayyar kasar Sin a Afirka tsawon shekaru 13 a jere. Ayyukan wutar lantarki bisa karfin iska da kamfanonin kasar Sin suka gina da ma gudanarwa a Afirka ta Kudu sun haskaka gidaje dubu 300 a yankin.

Afirka ta Kudu na daya daga cikin manyan wuraren zuba jari ga kasar Sin a nahiyar Afirka. A watanni 6 na farkon bana, yawan ciniki tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, ya karu da kashi 11.7 cikin 100 kan na shekarar bara.

Kamar yadda aka tsara, yayin taron kolin BRICS, shugabannin kasashen Sin da Afirka ta Kudu, za su jagoranci taron shugabannin kasashen Sin da Afirka. Wannan ya kara tabbatar da cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu suna son kafa wani dandalin zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka, da sa kaimi ga bunkasuwar masana'antu da dunkulewar nahiyar Afirka, da taimakawa kasashe masu tasowa na duniya samun ci gaba tare. (Ibrahim)