logo

HAUSA

Don me Japan ta keta al’adunta na yabawa teku ta zubawa masa ruwan dagwalon nukiliya?

2023-08-23 15:22:25 CMG HAUSA

DAGA MINA

Mene ne ma’anar teku ga Japanawa? Kasar Japan ke fuskantar teku a bangarori hudu, sun kirkiro “ranar teku” don bayyana muhimmancinsa, tare da bayyana fatansu na samun bunkasuwar kasar. Tun lokacin Jomon na tarihin yankin, Japanawa na da alaka da teku. A bangarorin daban-daban na rayuwarsu suna da mu’ammala matuka da teku, mai zana hoto da ya yi suna sosai a duniya Katsushika Hokusai, ya kwashe duk rayuwarsa yana zana teku, don bayyana kaunar Japanawa ga teku.

Amma, duk da cewa Japanawa na jinjinawa da yabawa teku a zuciyarsu, gwmanatin Japan ta yanke shawarar zubawa masa ruwan dagwalon nukilya. Wannan ruwan da aka sarrafa na cike da abubuwan guba ciki hadda Tritium, carbon-14, cobalt 60, strontium 90 da sauransu, da wuya ne za a kawar da su. To, mene ne dalilin da ya sa gwamnatin Japan ta keta al’adunta na yabawa teku ta zubawa masa ruwan?

Ba shakka, moirya ce. Ajiye wadannan ruwan zai kashe kudade da dama, amma zuba su a cikin teku na da araha. Dole ne gwamnatin Japan ta dudduba zuciyarta ta yi watsi da shirin a maimakon yunkurin fitar da matakan ba da kariya ga shirinta, da kuma yin hadin kai da sauran kasashe don kiyaye muhallin teku, ta yadda za su kiyaye al’adunsu. (Mai zana da rubuta:MINA)