Yadda fafada mambobin BRICS zai taka rawa a harkokin kasa da kasa
2023-08-23 09:13:19 CMG Hausa
Yanzu haka shugabanni ko wakilan kasashe mambobin kungiyar BRICS da suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya da Sin da Afirka ta kudu sun hallara a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halartar taron shugabannin kasashen kungiyar karo na 15.
A yayin taro na wannan karo, ana sa ran tattauna batun fadada ko kara yawan mambobin kungiyar, ciki har da batun ka’idodjin shiga kungiyar. Bayanai sun nuna cewa, BRICS ta zama wani muhimmin karfi a harkokin kasa da kasa.
Ya zuwa yanzu kasashe kusan 22 sun nuna sha’awarsu ta shiga kungiyar, duk da kalubale da saue-sauye da duniya ke fuskanta a halin yanzu. Kasashe mambobin kungiyar, galibi masu tasowa sun bayyana kudurinsu na hada kai don ciyar da ruhin kungiyar gaba. Tsarin BRICS yana goyon bayan daidaiton kasashe, da cudanyar bangarori daban-daban, da nuna adawa da yakin cacar-baka, da goyon bayan tsarin bude kofa don samun moriyar juna, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.
Haka kuma tsarin BRICS, yana kokarin samar da yanayin da ya dace ga kasashe masu tasowa a fannonin siyasa da tattalin arziki. Bayanai na nuna cewa, kasashe da dama sun gaji da babakeren Amurka a fannin tattalin arzikin duniya na tsawon lokaci, da tilasta musu bin wasu sharudda ko umarni kafin a ba su rance, wanda kin yin hakan na iya kaiwa ga sanya musu takunkumai.
Sama da kasashe 70 ne ake sa ran za su halarci taron na bana. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)