logo

HAUSA

Shiga tsarin BRICS wata babbar dama ce ta bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa

2023-08-23 17:25:44 CMG Hausa

Yanzu haka birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu ya dauki harami, inda shugabanni ko wakilan kasashen BRICS, da suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta kudu, suke gudanar da taron kolin shugabannin kungiyar karo na 15.

Wannan dai shi ne karo na biyu da nahiyar Afirka ke karbar bakuncin taron kungiyar. Ana sa ran taron na bana zai kasance mafi girma, inda aka gayyaci shugabanni kusan 69.

Manufar kungiyar dai ita ce, sake fasalin yanayin tattalin arziki da siyasa na kasashe mambobin kungiyar, inda suka kirkiro majalisar kasuwanci ta BRICS, yarjejeniyar bayar da tallafi na gajeren lokaci, da sabon bankin raya kasa wanda ke tallafawa ayyukan raya kasa a kasashen kungiyar.

Haka kuma taron na bana, wanda zai gudana daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta, zai mayar da hankali wajen rage dogaro kan dalar Amurka da ma yadda kasar ta Amurka ke yin babakere a harkokin kudi na duniya. Sauran fannonin sun hada da kara fadada wakilcin kungiyar, da tsarin cinikayya tsakanin kasashen kungiyar.

Bayanai sun nuna cewa, yanzu haka sama da kasashe 40 sun bayyana aniyarsu ta shiga kungiyar, har ma 22 daga cikinsu sun gabatar da bukatarsu a hukumance. Wannan ya kara tabbatar da karuwar tasirin kungiyar a harkokin kasa da kasa da ma karfinta na sake fasalta harkokin kudi a duniya a nan gaba.

Masu fashin baki na cewa, yadda karin kasashe ke fatan shiga kungiyar, hakika zai ba su damar kara cin gajiya a fannin tattalin arziki da cinikayya fiye da tsarin da kasashen yamma ke amfani da shi a halin yanzu.

BRICS ta zama wata dama ko zabi ga musamman kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da takwarorinsu kasashe masu tasowa, maimakon dogaro kan tsari ko hukumomin kudi na kasashe yammacin duniya, kamar bankin duniya ko IMF da makamantansu masu cike da danniya da babakere, don haka wannan wata babbar dama ce, abin ke zama tamkar maganar malam Bahaushe wato, Gida biyu maganin gobara.

Sai dai masharhanta na gargadin kar a yi kitso da kwarkwata, a lokacin da aka bayar da damar shigar wasu kasashe cikin kungiyar, domin kar su fake da wata mummunar manufa ko zama ’yan kanzagin kasashen yamma da nufin yiwa kungiyar zagon kasa. (Ibrahim Yaya)