logo

HAUSA

An gudanar da bikin fina-finan kasar Sin a Lagos na Najeriya

2023-08-23 10:44:19 CMG Hausa

A matsayin wani muhimmin mataki na karfafa hadin gwiwa da mu'amala a fannin zamantakewa karkashin tsarin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, an bude bikin fina-finai na kasar Sin da yammacin ranar 21 ga wata a birnin Lagos, babban birnin tashar jiragen ruwa ta Najeriya.

A jawabinsa na bude taron, mataimakin shugaban hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin Mao Yu, ya bayyana cewa, Najeriya kasa ce da ta jima da wayewa a nahiyar Afirka, kuma albarkatun da take da su a fannin tattalin arziki, zamantakewa, da al'adu sun samar da wata hanyar kirkire-kirkire ga masu shirya fina-finai na Najeriya. Yana fatan kasashen Sin da Najeriya za su iya amfani da wannan bikin na fina-finai a matsayin mafari, don ci gaba da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a fannin fina-finai, da sanya kuzari wajen raya kasuwar fina-finai ta duniya, da bayar da sabbin gudumawa wajen inganta gina al'umma mai makomar bai daya ga Sin da Afirka.

Shugaban kwamitin kula da fasaha da al'adu ta Najeriya NCAC Otunba Olusegun Runsewe, ya bayyana cewa, kasashen Najeriya da Sin suna da kyawawan al'adun gargajiya. Abin farin ciki ne a dauki wannan bikin na fina-finai a matsayin wata dama ta hada kan al’ummar Najeriya da kasar Sin, fim hanyar sadarwa ce da kowa ke fahimta a duniya. (Yahaya)